122 YADDA AKE YIN CHICKEN BALLS IN BUTTER

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

122 YADDA AKE YIN CHICKEN BALLS IN BATTER

Kayan Hadi:

 1. Tsokar Kaza
 2. Fulawa
 3. Baking powder
 4. Kwai
 5. Maggi
 6. Gishiri
 7. Mai
 8. Madara
 9. Koren tattasai
 10. Albasa,
 11. Citta

YADDA AKEYI

Zaki dafa kaza da magi da gishiri da garin citta da albasa ta dahu sosai, sai ki zare kashin a daka tsokar a turmi, ki aje agefe, sai ki yanka albasa da koran tattasai kanana, sai ki kwaba fulawa da baking powder ko kuma ita kadai duk yadda kikayi zeyi, amma kamar kwabin waina, sai ki dauko hadin nan na kaza da kwai madara koran tattasai magi da gishiri ki cakudasu har komai ya hadu idanma kina son attaruhu kina iya sawa, saiki cuccurata kamar yadda kika gani a hoto.

Sai ki dinga tsomawa fulawa kina soyawa, sai aci.

Cibiyar Bincike Da Wayar Da Kan Al’umma Akan Shafukan Yanar Gizo-Gizo Ta Sharfadi.com Ta Samar Da Wannan Dandalin Domin Amfanar Al’ummarmu.