118 YADDA AKE YIN WAINAR SHINKAFA

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

118 YADDA AKE YIN WAINAR SHINKAFA

Kayan Hadi:

  1. Shinkafa danya ta tuwo Shinkafan dafawa.
  2. Hanta
  3. Tattasai,
  4. Peace,
  5. Carrot,
  6. Ungurnu,
  7. Suga,
  8. Gishiri,
  9. Man gyada

Yadda Ake Yi:

Da farko zaki samu shinkafanki danya ta tuwo misali zaki na tiya daya ne, saiki jika ta a ruwa ta samu gud 2 or 3hours, sai ki samu shinkafan dafawa gwangwani 2 ki dafa, sai ki tsame waccan shinkafan ki wanke ki hada da wanda kika dafa, ki zuba yeast kadan ki bayar a kai miki nika, amma ki tabbatar ba’a cika miki ruwa ba, ko kuma ki bada wani abu kice a wanke miki a wani roban, shi kuma wancan kar a saka miki ruwa, in an kawo ki rufe ki manta dashi har zuwa washe gari, misali zakiyi na rana ne sai ki hada da yamma ya kwana anaso ya saki jikin shi ne sosai, saiki dauko idan zaki soya ki kankare carrot dinki ki yayyanka kanana ki hadada peace ki tafasa su shima hanta ki yanka kanana ki dafa ya dahu, sai ki yayyanka tattasan shima ki hada su wuri guda ki dauko kullun ki zuba mishi ruwan nan da aka wanke miki a gun nika sai ki zuba a ciki karki cika ruwa da dan kauri kadan ake so sai ki samu ruwan ungurnu ki zuba ki juya ki dandana in babu tsami to in kuma da tsami haka zaki ta sawa har kiji ba tsami sai ki zuba suga yanda kike bukata da gishiri ki dauko baking powder ki zuba dan ya kara taushi sai ki zuba mangyada a ciki dan ya kara shining sai ki zuba sauran kayan da kika yanka din nan in kinada bukata har albasa zaki yanka ki zuba sai ki nemi tanta ta karfe tafi kyau dama an hora ta sai ki hada wuta karki cika wuta dan baya zai soyu ciki bai soyu ba, kadan kadan anfi son garwashi sai a daura tanda in yai zafi ki yaryada man gyada in yai zaki ki zuba kullun sai ki barshi in yayi zaki gane ke da kanki sai ki nemi cokali ki juya can ma yayi haka haka har ki gama ki nemi abin zubawa amma ki yaji jarida ko takadda ki saka a kasa kafin ki fara saka wainar in kin gama ki dora wani takaddan a sma kamin ki refe maganin jikewa sai a hada da miya aci.