115 YADDA AKE YIN POTATO PIDDING

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

115 YADDA AKE YIN POTATO PIDDING

Kayan Hadi:

  1. Dankalin turawa
  2. Alayyahu
  3. Albasa
  4. Tattasai
  5. Citta dakakkiya
  6. Kifin gwangwani (sadin)
  7. Gishiri
  8. Maggi
  9. Leda

Yadda Ake Yi:

A yanka dankalin turawa kanana sosai, sai a tafasa shi da gishiri kadan (kada a bari ya dahu sosai) sai a zuba a matsami a tsane, sai a juye dankalin a kwano sai a kada kwai kamar shida ko bakwai dan ana son ya fito sosai, sannan a juye a kan dankalin daga nan a farfasa kifin a saka a ciki harda man sai a zuba yankakken attaruhu da albasa da alayyahu da maggi da gishiri da citta dan rage karni, in kina bukata da tafarnuwa sai ki juya ya hade .sannan ki samu leda ki dunga zubawa kina kullawa kaman zakiyi alala, sai ki dafa cikin ruwan zaki yanda ake alala, in ya dahu ki cire ledar, zaki iya cin sa da miyan tumatir (stew) ko jajjagen kayan miya.

Cibiyar Bincike Da Wayar Da Kan Al’umma Akan Shafukan Yanar Gizo-Gizo Ta Sharfadi.com Ta Samar Da Wannan Dandalin Domin Amfanar Al’ummarmu.