114 YADDA AKE YIN KOSAN SEMOVITA

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

114 YADDA AKE YIN KOSAN SEMOVITA

Kayan Hadi:

  1. Semovita
  2. Kwai
  3. Nama ko kifi
  4. Albasa
  5. Attaruhu
  6. Man gyada
  7. Maggi
  8. Gishiri
  9. Yeast
  10. Curry

Yadda Ake Yi:

Zaki kwaba semovitanki da yeas kamar zakiyi fanke kibarshi ya tashi, sai ki jajjaga albasa attaru ki aje gefe, sannan ki daka dafaffan namanki ko kifi ki hada dasu attaruhu ki ajiye, ki dafa kwai ki yayyanka sannan ki fasa wani ki ajiye, ki dauko kullun nan ki duba ko ya ttashi idan ya tashi sai ki zuba wadannan kayan duka a ciki tare da curry maggi da gishiri ki juya sosai.

Sai ki dora mai a kan wuta kamar zakiyi kosai ki dinga diba kina zubawa idan da wutama zakiga yana juyawa dakansa ba sai kin juyaba, sai a kwashe za a iyaci da kunun shinkafa ko na shi semovita din ko kuma wanda kike so.

Cibiyar Bincike Da Wayar Da Kan Al’umma Akan Shafukan Yanar Gizo-Gizo Ta Sharfadi.com Ta Samar Da Wannan Dandalin Domin Amfanar Al’ummarmu.