112 YADDA AKE YIN KUNUN SHINKAFA

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

112 YADDA AKE YIN KUNUN SHINKAFA

Kayan Hadi:

  1. Shinkafa gwangwani 2
  2. Madara peak 1
  3. Sukari
  4. Kwakwa 1

Yadda Ake Yi:

Zaki wanke shinkafarki ki bayar a markado miki ki tace sannan ki bare kwakwarki ki kankare bakin bayanta ki gogata a abin goga {kubewa} amma kanana sai ki dora tukunya a murhu ki zuba ruwa yadda zai yi miki.

Sai ki kawo kwakwar nan ki zuba a ciki su tafaso tare idan bakyason citon zaki iya kwashewa amma dashi yafi dadi, saiki kawo kullun nan ki dama kamar kunu, idan kina son lemon tsami zaki iya sa dan kadan, sai ki sa suga da madara ki juye a flas.

Cibiyar Bincike Da Wayar Da Kan Al’umma Akan Shafukan Yanar Gizo-Gizo Ta Sharfadi.com Ta Samar Da Wannan Dandalin Domin Amfanar Al’ummarmu.