108 YADDA AKE YIN FUNKASO

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

108 YADDA AKE YIN FUNKASO

Kayan Hadi:

  1. Fulawa
  2. Flkama
  3. Ruwa
  4. Kanwa
  5. Yis
  6. Mai
  7. Wake

Yadda Ake Yi:

Ki tankade garin alkama ko fulawarki, ko kuma ki hada duka idan na rabi rabi zakiyi sai ki sa garin alkama gwangwani biyu fulawa gwangwani biyu idan kina son wake sai kisa rabin gwangwani a niko miki tare xe kara laushin sa, sai ki kwaba da yis kamar kwabin fanke ki aje shi zai kumburo inya tashi sai ki buga shi sosai sai ki dansa kanwa, sai ki dora mai a wuta ki dinga gutsirar kullun kina fadadawa a bayan faranti ki huda tsakiyarsa ki sa a mai ki soya idan yayi ja ki tsame, zaki iya hadawa da farfesu.

Cibiyar Bincike Da Wayar Da Kan Al’umma Akan Shafukan Yanar Gizo-Gizo Ta Sharfadi.com Ta Samar Da Wannan Dandalin Domin Amfanar Al’ummarmu.