107 YADDA AKE YIN SPICY MEAT

Domin cigaba da samun sababbin rubutukanmu kayi subscribing din mu da Email dinka Shiga nan kayi like din shafinmu ta Facebook Shiga nan kayi following dinmu ta Instagram Shiga nan kayi following dinmu ta Twitter Shiga nan kayi subscribing dinmu ta YouTube

107 YADDA AKE YIN SPICY MEAT

Kayan Hadi:

  1. Nama
  2. Mai
  3. Tafarnuwa
  4. Gishiri
  5. Maggi
  6. Curry
  7. Kwai
  8. Attaruhu
  9. Albasa

Yadda Akeyi:

Ki markada danyan namanki mara kitse a blander tare da albasa curry maggi gishiri da tafarnuwa, idan kina son attaru zaki iya sawa amma in bakya so ba dole bane saboda akwai masu (ulcer), ki zuzzuba a leda ki kulle kamar alala ki zuba a tukunya ki dafa idan yayi kamar minti 30 sai ki sauke sai ki cireshi daga ledar zakiga ya cure sai kiyi masa yankan da kike so sai ki fasa kwai kisa magi ki4 kada ki dinga tsomawa a kwan kina soyawa zaki iya ci da komai.